Matthew 25

Misali na Budurwai Goma

1“A lokacin mulkin sama zai zama kamar budurwai goma waɗanda suka ɗauki fitilunsu suka fita don su taryi ango. 2Biyar daga cikinsu wawaye ne, biyar kuma masu hikima. 3Wawayen sun ɗauki fitilunsu, sai dai ba su riƙe mai ba. 4Masu hikimar kuwa suka riƙo kwalaben mai da fitilunsu. 5Ango ya yi jinkirin zuwa, sai duk suka shiga gyangyaɗi har barci ya kwashe su.

6“Can tsakar dare, sai aka ji kira, ana cewa, ‘Ga ango nan! Ku fito, ku tarye shi!’

7“Sai dukan budurwan nan suka farka suka kuna fitilunsu. 8Sai wawayen suka ce wa masu hikimar, ‘Ku ɗan sassam mana manku; fitilunmu suna mutuwa.’

9“Su kuwa suka amsa, suka ce, ‘Aʼa, wataƙila ba zai ishe mu da ku ba. Gara ku je wurin masu sayarwa ku sayo.’

10“Amma yayinda suke kan tafiya garin sayen mai, sai ango ya iso. Budurwai da suke a shirye, suka shiga wajen bikin auren tare da shi. Aka kuma kulle ƙofa.

11“An jima can, sai ga sauran sun iso. Suka ce, ‘Ranka yǎ daɗe! Ranka yǎ daɗe! Ka buɗe mana ƙofa!’

12“Amma ya amsa, ya ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, ban san ku ba.’

13“Saboda haka sai ku zauna a faɗake, don ba ku san ranar ko saʼar ba.

Misali na Talenti

14“Har wa yau, za a kwatanta shi da mutumin da zai yi tafiya, wanda ya kira bayinsa ya kuma danƙa musu mallakarsa. 15Ga guda, ya ba shi talentii biyar na kuɗi, ga wani talentii biyu, ga wani kuma talentii ɗaya, kowa bisa ga azancinsa. Saʼan nan ya yi tafiyarsa. 16Mutumin da ya karɓi talentii biyar, nan da nan ya tafi ya yi kasuwanci da su har ya sami ribar talentii biyar. 17Haka ma, wannan mai talentii biyu, shi ma ya yi riba biyu. 18Amma mutumin da ya karɓi talentii ɗaya ɗin, ya tafi, ya tona rami, ya ɓoye kuɗin maigidansa.

19“Bayan an daɗe, sai maigidan bayin nan ya dawo, ya kuma daidaita lissafi da su. 20Mutumin da ya karɓi talentii biyar, ya kawo ƙarin talentii biyar. Ya ce, ‘Maigida, ka danƙa mini talentii biyar. Ga shi, na yi ribar biyar.’

21“Maigidansa ya amsa, ya ce, ‘Madalla, bawan kirki mai aminci! Ka yi aminci a kan abubuwa kaɗan, zan sa ka lura da abubuwa masu yawa. Zo ka yi farin ciki tare da maigidanka!’

22“Mutumin da yake da talentii biyu, shi ma ya zo, ya ce, ‘Maigida, ka danƙa mini talentii biyu; ga shi, na yi ribar biyu.’

23“Maigidansa ya amsa, ya ce, ‘Madalla, bawan kirki mai aminci! Ka yi aminci a kan abubuwa kaɗan, zan sa ka lura da abubuwa masu yawa. Zo ka yi farin ciki tare da maigidanka!’

24“Saʼan nan mutumin da ya karɓi talentii ɗaya ya zo. Ya ce, ‘Maigida, na san cewa kai mutum ne mai wuyan shaʼani, kana girbi inda ba ka shuka ba, kana kuma tara inda ba ka yafa iri ba. 25Saboda haka na ji tsoro, na je na ɓoye talentiinka a ƙasa. Ga abinka.’

26“Maigidansa ya amsa, ya ce, ‘Kai mugun bawa, mai ƙyuya! Ashe, ka san cewa ina girbi inda ban yi shuka ba, ina kuma tarawa inda ban yafa iri ba? 27To, in haka ne, ai, da ka sa kuɗina a banki, don saʼad da na dawo da na karɓi abina da riba.

28“ ‘Karɓi talentiin daga hannunsa ku ba wanda yake da talentii goma. 29Gama duk mai abu za a ƙara masa, zai kuma same shi a yawalce. Duk wanda ba shi da shi kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai an karɓe masa. 30Ku jefar da banzan bawan nan waje, cikin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.’

Tumaki da Awaki

31“Saʼad da Ɗan Mutum ya zo cikin ɗaukakarsa, tare da dukan malaʼiku, zai zauna a kursiyinsa cikin ɗaukakar sama. 32Za a tara dukan alʼummai a gabansa, zai kuma raba mutane dabam dabam yadda makiyayi yakan ware tumaki daga awaki. 33Zai sa tumaki a damansa, awaki kuma a hagunsa.

34“Saʼan nan Sarki zai ce wa waɗanda suke damansa, ‘Ku zo, ku da Ubana ya yi wa albarka; ku karɓi gādonku, mulkin da aka shirya muku tun halittar duniya. 35Gama da nake jin yunwa, kun ciyar da ni, da nake jin ƙishirwa, kun ba ni abin sha, da nake baƙunci, kun karɓe ni, 36da nake bukatar tufafi, kun yi mini sutura, da na yi rashin lafiya, kun lura da ni, da nake kurkuku, kun ziyarce ni.’

37“Saʼan nan masu adalci za su amsa masa, su ce, ‘Ubangiji, yaushe muka gan ka da yunwa muka ciyar da kai, ko da ƙishirwa muka ba ka abin sha? 38Yaushe kuma muka gan ka baƙo muka karɓe ka, ko cikin bukatar tufafi muka yi maka sutura? 39Yaushe kuma muka gan ka cikin rashin lafiya ko a kurkuku muka ziyarce ka?’

40“Sarkin zai amsa, ya ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, duk abin da kuka yi wa ɗaya daga cikin waɗannan ʼyanʼuwana mafi ƙanƙanta, ni kuka yi wa.’

41“Saʼan nan zai ce wa waɗanda suke a hagunsa, ‘Ku rabu da ni, laʼanannu, zuwa cikin madawwamiyar wutar da aka shirya don Iblis da malaʼikunsa. 42Gama da nake jin yunwa, ba ku ba ni abinci ba, da nake jin ƙishirwa, ba ku ba ni abin sha ba, 43da na yi baƙunci, ba ku karɓe ni ba, da nake bukatar tufafi, ba ku yi mini sutura ba, da na yi rashin lafiya kuma ina a kurkuku, ba ku lura da ni ba.’

44“Su ma za su amsa, su ce, ‘Ubangiji, yaushe muka gan ka cikin yunwa ko ƙishirwa ko baƙo ko cikin bukatar tufafi ko cikin rashin lafiya ko cikin kurkuku, ba mu taimake ka ba?’

45“Zai amsa, yǎ ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, duk abin da ba ku yi wa ɗaya daga cikin waɗannan mafi ƙanƙanta ba, ba ku yi mini ba ke nan.’

46“Saʼan nan za su tafi cikin madawwamiyar hukunci, amma masu adalci kuwa za su shiga rai madawwami.”

Copyright information for HauSRK